18 Afirilu 2021 - 13:55
Rasha: Tace Sanadarin Uranium Da Ya Kai Daraja 60 % Da Iran Ta Yi Zai Yi Tasiri Mai Kyau A Tattaunawar Nukiliya A Vienna

Shugaban cibiyar samar da makamashi da kuma tsaron kasar Rasha, Anton Khlopkov ne ya bayyana cewa yadda Iran din ta yi nasarar tace uranium da daraja 60%, zai yi tasiri a tattaunawar kwamitin hadin gwiwa na yarjejeniyar Nukiliya a Vienna.

ABNA24 : Anton Khlopkov wanda jaridar Kamresanet ta kasar Rasha ta yi hira da shi ya kara da cewa; Matakin na Iran zai iya sanya Amurka ta daina jan kafar da take yi, domin daukar matakan siyasar da za su kai ga cimma yarjejeniya.

A jiya Asabar ne dai aka bude tattaunawar kwamitin hadin gwiwa na yarjejeniyar Nukiliya a birnin Vienna wanda ya sami halartar Iran da saukar kasashen suke cikin yarjejeniyar. A yayin tattaunawar ta jiya an yi bitar sakamakon tarukan da aka yi a baya, da kuma batun dauke wa Iran din takunkuman da aka kakaba mata.

342/